Yahudawa yan share wuri zauna 3 ne suka halaka a yayinda wasu 7 suka ji rauni a musayar wuta tsakaninsu da Falasdinawa a kusa da garin Kedumin na yahudawa a yankin yamma da kogin Jordan.
Kamfanin dollancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, wasu hotuna wadanda aka yada a shafukan sadarwa sun nuna wani mutum yana harbi kan wata motar Bus da kuma wasu kananan motoci 2 a unguwar Al-Funduq cikin garin Kedumin na yankin yamma da kogin Jordan.
Likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane 3, biyu mata da wani na miji sannan hukumar bada agajin gaggawa ta ‘Magen David Adon’ ta tabbatar da labarin.
Majiyar gwamnatin HKI ta bayyana cewa sijijin kasar sun fara bincike gida gida don gano wadanda suka aikata kissan a unguwar ta Al-funduq .