Wata mujallar kiwon lafiya a kasar Burtaniya ta bayyana cewa mai yuwa sojojin HKI sun kashe falasdinawa kimani dubu 186 a Gaza tun fara yaki a Gaza watanni 9 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mujallar kiwon lafiya ‘The Lancet’ tana fadar haka a wani rahoton da aka buka a cikinta a ranar Jumma’an da ta gabata.
Mujallar ta kara da cewa a lissafinta da ta yi, wanda kuma ya hada da falasdinawa da aka kashe kai tsaye da makaman sojojin HKI, da kuma wadanda suke bisne a karkashin kasa da kuma wadanda yunwa ta kashe da sauransu zai kai wannan adadin. Adadin da hukumar lafiya a Gaza take bada rahotonsa ya ninka adadin har sau 4 idan an hada da wannan lissafin.
Don haka idan an dauki wasu Karin hanyoyi 4 da jaridar ta ambata, da sojojin HKI suke kashe zai kai dubu 186.
Masana da dama dai suna ganin cewa cikekken adadin Falasdinawa da sojojin HKI suka kashe a Gaza, zai bayyana ne kawai bayan an kawo karshen yakin, sannan aka gudanar da cikekken bincike kan wadanda suka bace, ko aka tabbatar da cewa suna karkashin gine ginen da aka rugurguza a kansu.
Kissan kiyashin da HKI take aikawa a gaza dai ya tada hankalin mutane da dama a duniya, daga cikin har da hukumomin MDD. Amma kuma an kasa samun wanda zai tsawatawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin.
Kasashen yamma musamman Amurka suna daga cikin kasashen da suke tallafawa yahudawan a kissan kiyashin da suke a gaza.