Kungiyar kare hakkin bil-adama ta – The Euro-Mediterranean Human Rights Monitor ta bukaci a hukunta gwamnatocin Amurka da HKI kan shirin rabon abincin da suke gudanarwa a gaza, wanda ya kai ga mutuwar Falasdinawa da dama.
Kungiyar ta bayyana cewa kasashen biyu sun hada kai don fiyar da falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a cikin gaba, a inda sojoji HKI zata kashe su. Kungiyar ta bukaci a gaggauta binciken manufar wannan shirin, wanda manufarta ita ce fitar da falasdinawa wadanda hana abinci fita don su kashesu.
Rahoton ya kara da cewa, misali guda shi ne abinda ya faru a yankin Ash-shakoush inda sojoijin HKI suka kashe falasdinawa akalla 30 wadanda suka fito don karban abinci. Sannan suka raunata wasu 180.
HKI tare da Amurka sun hana abinci shiga Gaza ta kofar Rafah da kuma Kerin Abu saleh na tsawon watanni, har sai da Falasdinawa bas u da zabi ko sum utu yunwa ko kuma su fito karban abinci inda sojojin yahudawan zasu samesu su kashe su a kan abincin da ba zasu ci ba.