Wata kungiyar kwararru maku kare abinda suka kira Domocradiyya a duniya ta bayyana damuwarta da yaduwar makaman ‘Drone’ na JMI a kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran IRNA na cewa makaman kasar Iran musamman jiragen kunan bakin wake da kuma na leken asiri sun watsu a kasashen duniya kama da Ukrai zuwa HKI da kuma Sudan.
Labarin ya kara da cewa kasar Iran ta cika yankin gaban ta tsakiya da makamanta wadanda mai yuwa nan gaba su zama masu bada kariya ga wadannan kasashe. Ya kara da cewa a kasar Rasha kadai tun bayan fara yaki a Ukraine sun kiyast cewa kasar Rasha ta yi amfani da makaman Drone ko kuma jiragen yaki masu konan bakin wake wadanda kuma ake sarrafasu da nesa har 2600.
Sannan Iran kanta ta yi amafani da irin wadannan makamai kan HKI a farkon wannan shekarar. Kungiyar ta bayyana cewa makaman suna da matukan hatsari ga sojojin Amurka da kawayensu a yankin ghabas ta tsakiya. Kuma Iran ta koyawa kasar Venezuela aikin kera wadan nan makamai a gida.
Kungiyar kare Democradiyya ta Amurka ta kara da cewa jirgin yakin day a fara kai hare hare kan birnin Tel-aviv a kwanakin baya, ya ratsa tazaran kilomita 2600 kafin ya fada kan tel’aviv.