Mambobin majalisar dokokin Birtaniyya sun soki yadda gwamnatin kasar ta gaza wajen tunkarar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ke kai hare-hare a wuraren musulmi ta hanyar yada kiyayya ga musulmi.
A rahoton Yeni Shafaq, ‘yan majalisar dokokin Burtaniya da dama sun soki yadda gwamnatin kasar ke nuna halin ko in kula dangane da tarzomar kyamar musulmi.
Jeremy Corbyn, tsohon shugaban jam’iyyar Labour ta Biritaniya, da wasu ‘yan majalisa hudu masu zaman kansu, sun ce abin damuwa ne yadda gwamnati ba ta da wani shiri na ganawa da jami’an Majalisar Musulmi ta Birtaniyya, a daidai lokacin da gungun masu nuna wariya ke kai hari kan masallatai da cibiyoyin ‘yan gudun hijira.
Sun caccaki Fira Minista Keir Starmer bisa rashin daukar matakai na tunkarar tarzomar masu tsatsauran ra’ayi a baya-bayan nan, suna masu zargin gwamnatin kasar da gazawa wajen magance kyamar baki da musulmi da ke kara ruruwa a cikin kasar.
A cikin wata wasika, ‘yan majalisar sun bayyana rashin jin dadinsu da martanin da Mr Starmer ya mayar ga masu zanga-zangar masu ra’ayin mazan jiya da suka tayar da tarzoma a garuruwan Burtaniya a karshen makon da ya gabata. Sun ce gwamnati ba ta yin abin da ya dace wajen magance abubuwan da suke jawo kiyayya da ke haddasa tashe tashen hankula ba.
A cikin wasikar da suka rubuta wa Yvette Cooper, sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya, wadannan wakilan sun soki lamirin gwamnatin kasar da kuma matsayar da ta dauka da bai dace ba, da kuma rashin sanin muhimmiyar rawar da masu kyamar baki da musulmi suka taka, wajen tayar da wannan tarzoma.