A jiya Litinin Wasu ‘Yan Majalisar Dokokin Birtaniya sun yi kira da kasar tasu ta dakatar da kai wa Isra’ila makamai adaidai lokacin da yanayi yake kara tsanani a Gaza.
‘Yan majalisar da su ka fito daga jam’iyyu mabanbanta, sun taru a wajen ginin “Westminster” suna dauke da kyalle da aka rubutu cewa: “ A Daina Bai Wa Isra’ila Makamai.”
Ana kuma sa ran cewa a yau ne za a yi tattaunawa a cikin Majalisar ta Birtaniya akan batun makaman, bayan da wasu ‘yan kasar su 100,000 su ka yi kira da a soke lasisin sayar wa da Isra’ilan makamai.
A ranar Litinin da marece ne dai fiye da mutane 107,000 su ka sa hannu akan takardar yin kira a dakatar da sayarwa HKI makamai.
Wasu ‘yan majalisa su 60 sun rubuta wasikar da suke kira a cikinta akan sanya wa Isra’ila takunkumi. Sun kuwa kafa dalili ne da yadda Isra’ilan take take dokokin kasa da kasa a Gaza.
Wannan matakin dai ya biyo bayan da kotun kasa da kasa ta manyan laifuka dake birnin Hague ta bayar da sammacin kamo fira minitan HKI Benjamin Netanyahu da kuma ministansa na yaki Yoav Zgallant saboda laifukan yakin da su ka tafka a Gaza.