Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Wafa cewa: Wasu Falasdinawa uku sun yi shahada, wasu daban kuma suka samu raunuka sakamakon harin wuce gona da iri da jirgin saman yakin yahudawan sahayoniyya maras matuki ciki ya kai kan wasu fararen hula da suke gudanar da zanga-zangar lumana a kan titin Al-Sahaba da ke tsakiyar Zirin Gaza.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ruwa da kuma ta sama kan Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 37,124 tare da jikkata wasu 84,712, yayin da wasu dubban wadanda hare-haren suka shafa ke ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine, wasu miliyoyi kuma suka yi gudun hijira.
Agefe guda kuma, tun daga yammacin jiya Litinin zuwa safiyar yau Talata, sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kama falasdinawa akalla goma sha biyar a Yammacin Kogin Jordan, kuma ciki har da tsoffin fursunoni.