Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa a biranen El Fasher, Khartoum da Darfur
Rahotonni sun bayyana cewa: Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a wasu biranen Sudan tsakanin sojojin kasar da Dakarun kai daukin gaggawa a biranen El Fasher, Khartoum da Aljazira, inda Dakarun kai daukin gaggawa suka yi barin wuta da manyan bindigogi kan sojojin Sudan, yayin da sojojin Sudan suka yi luguden wuta da jiragen saman yaki kan yankunan da Dakarun kai daukin gaggawa suka mamaye a arewa maso maso gabashin birnin.
Garuruwan Sudan dai na fuskantar tashe tashen hankula na soji da dama tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa, inda ake amfani da manyan makamai, musamman jiragen saman yaki da manyan bindigogin yaki a garuruwan El Fasher, Khartoum, da kuma jihar Aljazira.
A cikin birnin El Fasher, dakarun kai daukin gaggawa sun kai munanan hare-hare kan rundunar sojojin kasar da manyan bindigogi, yayin da jiragen saman yakin sojojin Sudan suka yi ruwan bama-bamai kan yankunan da Dakarun kai daukin gaggawa suka mamaye a arewa maso gabashin birnin, yayin da birnin El Fasher ke fama da matsanancin halin jin kai bayan ya rikide zuwa fagen fama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan fararen hula.