Wani Mai Binciken Kan Harkokin Siyasa Ya Yi Zargin Akwai Hannun Wasu Kasashen Larabawa A Kutsen Irsa’ila A Siriya

Haramtacciyar kasar Isra’ila tana yin kutse cikin kasar Siriya ce da hannun wasu kasashen Larabawa Marubuci kuma mai bincike kan harkokin siyasa, Youssef Hazma, ya

Haramtacciyar kasar Isra’ila tana yin kutse cikin kasar Siriya ce da hannun wasu kasashen Larabawa

Marubuci kuma mai bincike kan harkokin siyasa, Youssef Hazma, ya jaddada cewa: Kasancewar yahudawan shayoniyya a cikin yankunan kasar Siriya yana nuni da cewa: Babu makawa akwai hannun wasu shugabanni a yankin Gabas ta Tsakiya da suke da masalaha wajen bai wa yahudawan sahayoniyya damar gudanar da shawagi a cikin kasar, yana mai cewa; A yau suna fuskantar wani yanayi da ke da nasaba da raba kasar Siriya tsakanin kasar Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma makwaftan Siriya daga bangaren Turkiyya.

Hazma ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da tashar talabijin ta Al-Alam ta kasar Iran yana mai cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila a ta bakin Netanyahu tana cewa: Ba za ta fice daga yankunan Siriya da ta sake mamayewa ba, hakan na nuni da cewa wannan sabuwar mamayar an gudanar da ita ce a gaban kasashen yammacin duniya, amma abin tambaya a nan ita ce: Ina kasashen Larabawa suke, kuma mene ne dalilin shirunsu kan tsoma bakin haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin harkokin Siriya?

Ya kara da cewa: Sabuwar gwamnatin Siriya ba ta dauki wani matakin yakar ‘yan mamaya ba, domin sabbin shugabannin kasar suna magana ce kan shirye-shiryensu da kuma jajircewarsu kan batun dakatar da yaki tsakanin Siriya da haramtacciyar kasar Isra’ila ne da aka amince da shi a ranar 31 ga Mayun shekara ta 1974 ce kawai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments