Wani Jariri Ya Rasa Ransa Saboda Sanyi A Gaza, A Lokacind Sojojin HKI Suka Kai Hari Kan Asbitin Al-Wafa A Tsakiyar Birnin Gaza

Wani jaririn falasdinawa ya mutu sanadiyyar tsananin sanyi a lokacinda sojojin yahudawan Isra’ila suka kai hari kan Asbitin Al-Wafa na tsakiyar birnin Gaza a safiyar

Wani jaririn falasdinawa ya mutu sanadiyyar tsananin sanyi a lokacinda sojojin yahudawan Isra’ila suka kai hari kan Asbitin Al-Wafa na tsakiyar birnin Gaza a safiyar yau Lahadi. Wannan bas hi ne karon farko inda jarirai suke mutuwa saboda sanyi a Gaza ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wata kungiyar agaji ta Falasdinawa ta na fadar haka a yau Lahadi.

Munir al-Barsh, wani darakta a ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza, ya bayyana cewa an sake gidan Asbitin bayan rusashi da sojojin HKI suka yi a bayan, kuma har ma ana fatan za’a sake bude shi a cikin yan makonni masu zuwa, amma hare-haren da sojojin yahudawan suka sake kaiwa kan asbitin a jiya ya maida hannun agogo baya.

Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadai da hare-hare kan asbitin Al-wafa, sannan ta kira shi da ‘laifin yaki’, sannan ta yi tir da shirun da kungiyoyi da hukumomin da abin ya shafa suka yi, dangane da hare-haren yahudawa a kan asbitocin da suka rage a Gaza. A halin yanzu dai shinya yana kashe jarirai a gaza saboda basa da wurin dumama jikinsu a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments