Jami’in Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Amurka tana yin kuskure a lissafimta kan kasar Iran
Shugaban kwamitin tsaron kasa da kare manufofin harkokin wajen Iran a majalisar shawarar Musulunci ta Iran, Ibrahim Azizi ya bayyana cewa: Kirdado da ayyukan kuskure da Amurka da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa musamman na kashe kananan yara lamari ne da ke kara zaburar da ‘yan gwagwarmaya wajen kara karfin gudanar da gwagwarmayar kare kansu da al’ummarsu daga duk wasu ayyukan wuce gona da iri da suke fuskanta.
Azizi ya kara da cewa, a yammacin jiya Alhamis, a wajen bikin tunawa da shahidan yankin birnin Dashtestan da ke lardin Bushehr a kudancin kasar Iran: A yau, yankin yammacin Asiya da yankin gabas ta tsakiya na samun ci gaba cikin sauri da wasu sarkakiya da kuma ci gaba da aka samu a wasu fagage. Duk da Amurka da kawayenta suna ci gaba da kaddamar da yakin wuce gona da iri bisa rudun tunanin neman maido da tsaro cikin jerin kakashe da aka mamaye.
Ya kara da cewa: Ta hanyar tayar da hargitsi a yankin da kuma amfani da dukkan karfinsu, suna kokarin maido da yankuna masu tsaro zuwa yankunan da suke karkashin da suka mamaye, yayin da kuma tatsuniyar cewa; “Isra’ila ba a galaba kanta” ta shiga mummunan firgici da rudu da rashin nutsuwa a yayin fuskantar harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” na ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa da harin “Alkawarin Gaskiya da Iran ta kai mata kan daukan fansan kisangillar da ta yi wa Isma’il Haniyah shugaban ofishin siyasar kungiyar gwagwarmayar Msusulunci ta Hamas.