Ma’aikatar lafiya ta Yemen ta ce wani harin da Isra’ila ta kai kan tashar jiragen ruwa ta Hudaidah, ya yi sanadin mutuwar fararen hula akalla uku tare da jikkata wasu 90.
Jami’an Yemen sun ce harin na ranar Talata ya auna wuraren ajiyar man fetur da kuma wata cibiyar samar da wutar lantarki a kudancin kasar.
Sojojin Isra’ila sun tabbatar da cewa jiragen yakinsu sun kai hari a Yeman.
Kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Ansarallah ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa matsin lamba wa kasar Yemen ta daina goyon bayan Gaza, abu ne mai wuyar gaske.
Kungiyar ta kuma ce Isra’ila za ta fuskanci martani kan harin .
Dama dai Isra’ila ta kai hari a wuraren ajiyar man fetur da kuma wata tashar samar da wutar lantarki a Hudaydah a ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata.
Akalla mutane tara ne suka mutu sannan wasu 87 suka jikkata a harin na waccen lokacin.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch (HRW) a ranar Litinin ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a tashar jiragen ruwa ta Hudaidah a watan da ya gabata wanda ta danganta a matsayin “laifin yaki.”