Wani babban hafsan sojan Amurka ya ajiye aikinsa domin nuna kyamarsa ga goyon bayan da kasarsa ke bai wa Isra’ila da ke kashe Falasdinawa.
Hafsan sojan mai mukamin Manjo, Harrison Mann, ya ce, goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra’ila na nufin tana jin dadin yadda ake cigaba da kisan gilla ga fararen hula a Falasdinu.
Murabus din Manjo Harrison Mann ya kara yawan manyan sojoji da jami’an gwamnatin Amurka farar hula da suka ajiye aiki domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa.
Haka na kuma kara nuna yadda suke kin jinin da cigaba da zaluntar Falsɗinawa da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza.
A cikin wata wasika da ta bayyana a ranar Litinin, Manjo Harrison Mann, ya bayyana wa abokan aikinsa a hukumar leken asiri ta DIA cewa, murabus din nasa a watan Nuwamban bara ya faru ne saboda yadda ya lura cewa an samu “lalacewar tarbiyya da gushewar tausayi”
Ya ce ya gano hakan ne daga irin goyon bayan da Amurka ke nuna wa Isra’ila a kan Falasindawa a Zirin Gaza.
“Wannan abin kunya ne a ganina, kuma laifi ne mai ban girma,” inda ake azabtar da kananan yara in ji Mannan wanda kakaninsa yahudawa na.
Mann ya ce abin da kasarsa ke yi babban laifi ne, don haka “dole a cikin biyu ya dauki daya, wato adawa ko kuma goyon bayan yadda ake azabtar d kananan yara da gallaza musu ko kuma a a, tun da yaran nan basu ji ba basu gani ba”.
A cikin wasikar ajjiye aikin ya ce “Ina so in bayyana muku cewa a matsayina na tsatson Yahudawan Turai, an tarbiyyantar da ni a kan sanin girman zunubin cin zali da kisan kare dangi.”