Wakiliyar Kasa Da Kasa A Falasdinu Ta Karyata Da’awar Faransa Cewa Netanyahu Yana Da Kariya                                                                                                                                                                               

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Falasdinu ta yi watsi da ikirarin kasar Faransa cewa fira ministan Isra’ila yana da kariya Wakiliyar Majalisar Dinkin

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Falasdinu ta yi watsi da ikirarin kasar Faransa cewa fira ministan Isra’ila yana da kariya

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Falasdinu, Francesca Albanese, ta yi watsi da da’awar da kasar Faransa ta yi na cewa Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benyamin Netanyahu na iya cin gajiyar kariya a karkashin dokokin kasa da kasa.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Albanese ta bayyana a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa: Irin wannan rigakafin ba shi da tushe na doka, tana mai cewa da’awar Faransa na cewa Netanyahu yana da kariya “ba karbabbe ba ne a bisa doka” ta kuma kara da cewa wannan matsayin “ba shi da mazauni a fagen doka.”

Wakiliyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma tabo batun tsohon shugaban kasar Sudan Umar Hasan Al-Bashir, duba da cewa kotun kasa da kasa ta warware batun kariyar da ke da shi tun da farko.

Albanese ta jaddada cewa: Duk wani yunkuri na neman hana aiwatar da sammacin kame da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar zai zama cin zarafi ga doka ta 70 na yarjejeniyar Roma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments