Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr
Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr dake kudancin kasar Iran.
A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na X, Ulyanov ya rubuta cewa: Iran ta sake tabbatar da cewa, ko da bayan hare-haren da sojoji suka kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarta na zaman lafiya da ke gudana karkashin hukumar ta IAEA ba bisa ka’ida ba, abin kunya ne, a matsayinta ta mamba ta hukumar ta IAEA.
A baya dai Abbas Araqchi ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa; shigar jami’an hukumar ta IAEA zuwa kasar Iran ya zo ne bisa ga umarnin kwamitin tsaron kasar na sa ido kan yadda ake sauya man fetur a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr, kuma babu wani hukunci na karshe na yarjejeniyar da aka cimma kan sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA.