Wakilin Falastinu A MDD ya bukaci daukar matakin dakatar da kisan kiyashi a Gaza

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin kawo karshen kisan

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin kawo karshen kisan kiyashin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza.

Da yake jawabi a gaban majalisar a ranar  Juma’an da ta gabata,  Mansour ya yin wani taro kan yankin Gabas ta Tsakiya, Mansour ya jaddada alhakin kasashen duniya na dakatar da abin da ya ke faruwa a Gaza.

Mansour ya ce, “Hakimmu ne mu kawo karshen wannan jahannamar da kisan kiyashi a kan mata da kananan yara, da tsoffi a Gaza, inda ya bukaci majalisar da ta sauke nauyin da ya rataya a kanta.

Zaman ya biyo bayan wani sumamen da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kan asibitin Kamal Adwan da ke yankin zirin Gaza, inda sojojin Isra’ila suka tsare shugaban asibitin Hussam Abu Safiyya.

Mansour ya bayyana halin da ma’aikatar lafiya ta  Falasdinu a gaza take ciki, da kuma yadda ayyukan  ceton rayuka a Gaza suka tsaya cik, saboda munanan hare-haren Isra’ila.

Mansour ya yaba da sadaukarwar da tawagogin likitocin Falasdinu ke yi, ya na mai cewa, “Suna gudanar da aikinsu ne a cikin wahala, amma duk da haka ba sa son mika wuya, domin sun yi rantsuwa a kan cewa zasu ci gaba da ayyukansu a ko wani hali suke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments