Wakilin Aljeriya A MDD Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Takaddamar Siyasa A Libya

Wakilin Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ammar Benjama, ya yi kira da a kawo karshen rarrabuwar kawuna na siyasa tsakanin  hukumomin Libya, da karfafa gwiwa

Wakilin Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ammar Benjama, ya yi kira da a kawo karshen rarrabuwar kawuna na siyasa tsakanin  hukumomin Libya, da karfafa gwiwa tsakanin manyan jam’iyyun da kuma share fagen gudanar da zaben kasa.

Wakilin din din din na kasar Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ammar Ben Jama, ya yi kira a madadin mambobin kungiyar “A3+” (Algeria, Mozambique, Saliyo da Guyana) da a  kawo karshen rarrabuwar kawuna na siyasa, tare da aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi a kasar Libiya karkashin inuwar MDD, da nufin kawo karshen rikicin siyasa a kasar.

Ben Jama , a cikin jawabinsa a lokacin zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa “Kungiyar A3+ tana maraba da nasarar da aka samu a zabukan kananan hukumomi 58, wanda ke wakiltar wani muhimmin al’amari  don tabbatar da zaman lafiya a Libya.

Wakilin na Aljeriya ya jaddada cewa, “Gudunwar Majalisar Dinkin Duniya na da muhimmanci wajen shimfida  cikakkiyar hanyar tattaunawa a kasar Libya, wanda hakan ke  a matsayin wani muhimmin mataki na warware batutuwan da har yanz ake takaddama a kansu.

Baya ga haka kuma da shirya zabukan kasa masu inganci da tsafta,  da kuma hada kan cibiyoyi da hukumomi na kasar,” yana mai yabawa shawarar tawagar UNSMIL mai alaka da farfado da harkokin kasa da kasa, tsarin siyasa da amincewa tsakanin jam’iyyu da kuma shirya hanyar da za a bi don zabukan kasa.

Dangane da kawo karshen wa’adin tawagar UNSMIL a watan Janairu mai zuwa, Ben Jama ya bayyana damuwarsa game da rashin samun ci gaba wajen nada sabon wakili na musamman, yana mai jaddada kiransa a madadin kungiyar “3A+” cewa rawar da tawagar take takawa tana da muhimmanci, kuma ya kamata a dauki mataki na gaba domin kaucewa bullar wata sabuwar matsala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments