Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba

Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa

Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18.

Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a, ciki har da harba makamai masu linzami a halin yanzu a kusa da ruwan Rasha.

Wakilin shugaban Amurka Donald Trump na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na daukar matakan kawo karshen yakin Ukraine ke gabatowa. Trump ne ya sanar da hakan, wanda ya yi barazanar sanyawa Moscow takunkumi idan ba ta bi bukatunsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments