Urdugan: “Idan Ba A Dakatar Da  Dodanniya Isra’ila  Cikin Sauri Ba Za Kone  Wannan  Yankin Da Ma Duniya

Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya bayyana Isra’ila da cewa dabbar daji ce mai hatsari wacce idan ba a taka mata birki ba, to

Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya bayyana Isra’ila da cewa dabbar daji ce mai hatsari wacce idan ba a taka mata birki ba, to kuwa za ya hargitsa yankin yammacin Asiya da kuma duniya.

Kamfanin dillancin labarun Antoli na kasar Turkiya ya ambato shugaban kasar ta Turkiya yana mayar da martani akan abinda yake faruwa a kasar Syria yana mai cewa;Ina son in sake daga murya in yi Magana gwari-gwari in jaddada cewa; Isra’ila wata gwamnati ce ta ta’addanci wacce ba ruwanta da bin doka,mai halayyar daba da nuna karfi.”

Haka nan kuma shugaban na kasar Turkiya ya ce; Isra’ila ba ta da wani aiki sai jefa wannan yankin cikin kogin jinni da hargitsi da rashin zaman lafiya.”

Urdugan ya ce; Isra’ila ta kai hare-hare a kan kasashe Lebanon, Yemen, da Iran tare da kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba,amma wannan bai ishe ta ba, ta kai wa makwabciyarmu Syria hari.”

Shugaban kasar ta Turkiya ya kara da cewa; Isra’ila ce babbar matsala a cikin wannan yanki, idan kuwa ba a yi sauri an kama wannan dodanniyar ba,to za ta kone wannan yankin da da duniya baki daya.

Har ila yau, Urdugan ya ce muna kan ganiyar daukar dukkanin matakan da su ka dace domin fuskantar duk abinda zai iya faruwa, muna kuma sake jaddada wajabcin kare hadin kan kasar Syria.

Urdugan ya ce; ko ba dade, ko bajima, duk wadnada su ka jingina da Isra’ila za su fahimci cewa sun yi kuskuren lissafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted