Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ya ce kashi 70 cikin 100 na makarantun UNRWA ‘sun lalace tun bayan da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin da take yi a yankin da akayi wa kawanta.
Philippe Lazzarini, kwamishinan janar na UNRWA ya rubuta a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa ana amfani da wadannan makarantun da har yanzu suke a matsayin mafaka ga iyalai da suka rasa matsugunansu.
“Ba za a iya amfani da su ba don koyarwa ba, Ba tare da tsagaita bude wuta ba, wanda hakan barazane ga rayuwar yaran nan gaba wadanda ko dai su shiga aikin karfi ko kuma su amsa kiran kungiyoyi masu dauke da makamai,” in ji Lazzarini.
Sama da yara 600,000 a zirin Gaza na cikin rudani kuma suna rayuwa a cikin baraguzan gine-gine a cikin mummunan harin da Isra’ila ke kaiwa, in ji babban jami’in hukumar MDD.
Hare-haren Isra’ila, wanda ya fara a watan Oktoban bara, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 40,738 tare da jikkata wasu sama da 94,000 galibi yara da kuma mata.