UNICEF : Yara 74 Isra’ila ta Kashe A Gaza A Makon Farko Na 2025

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa akalla yara 74 ne aka kashe a rikicin da Isra’ila ta

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa akalla yara 74 ne aka kashe a rikicin da Isra’ila ta yi a zirin Gaza a makon farko na shekarar 2025, wanda abun bakin ciki ne a fara sabuwar shekara ga kananan yara a yankin da aka yi wa kawanya.

A rahoto na baya bayan nan da ta fitar a ranar Laraba, UNICEF ta ce an samu asarar rayuka a cikin kwanaki takwas kacal, inda ta jaddada cewa rashin isasshen matsuguni, da yanayin lokacin sanyi, na haifar da hadari mai tsanani ga yaran a Gaza.

“Ga yaran Gaza, sabuwar shekara ta zo da karin rasa rayuka da wahala ga yara,” in ji Babban Darakta na UNICEF Catherine Russell.

Mme Russell, ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa don kawo karshen tashin hankalin.

Ta nuna matukar damuwa kan yawan yaran da aka kashe ko kuma suka rasa ‘yan uwansu a farkon wannan shekara.

Rikicin jin kai a Gaza ya kai wani mataki mai ban tsoro.

Tun bayan fara kisan kiyashin, Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 46,936, da suka hada da yara sama da 17,600, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments