A ranar Jumma’a ce gwamnatin kasar Uganda ta gabatar da alluran riga kafin cutar Ebola na gwaji a kasar mai sun mRNA wanda masana magunguna na cikin gida tare da hadin kai da kamfanin magunguna na Modema suka samar.
Shafin yanar gizo na Labarai Africa News ya ce cibiyar binciken cututtukan Virus ta kasa ” wato Uganda ​Virus Research Institute” ta bada labarin cewa ta samar da alluran tare da hadin kai da Modema, inda ta samar da virus na cutar wacce bata cutarwa don haras da jinin mutane fada da cutar. Inda har an sami nasara alluran zata taimaka kwarai.
Labarin yace jarraba alluran a kasar Uganda shi ne biyu, bayan wacce aka yi a kasar Canada a cikin watan Augustan da ya gabata kan manyan mutane masu shekaru tsakanin 18-65.
Hukumar lafiya ta duniya WHO tace tun bullar cutar na baya bayana kasar Congo ta kashe mutane fiye da 5,700 cikin mutane 11,000 da suka kamu da ita daga cikin watan Mayun da ya gabata.
Kasar Udanga dai ta samu nasarar takaita yaduwar cutar duk da cewa tana da kan iyaka mai yawa da kasar Demcradiyar Kwango. Sannan a cikin watan Augustan ta shelanta kawo karshen cutar bayan tabbatar da kamuwar mutane 20 kacal daita, tare da mutuwar mutane biyu da cikinsu.