Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa major Janaral Muhsen Reza’I a lokacin ganawarsa da takwarorinsa na kasar Iraqi ya bayyana cewa dangantakar tatttalin arziki dake tsakanin su a matsayin makwabtan juna dole ne a kareta kada a bari wasu yan kasashen wajen su rika tsoma baki aciki, adaidai lokacin da aka rufe wasu iyakokin kasar da ake harkar kasuwanci tsakani
Babban sakataren yayi wannan bayani ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar tsaron kasar Iraqi Qasim al-Aboudi a nan birnin Tehran a jiya asabar, yace iraki mai yanci da karfi wadda ta ci gaba za ta zama daya daga cikin ginshikai a bangaren tsaro a yankin baki daya
Kuma yayi wannan bayani ne adaidai lokain da rahotanni ke bayyana irin yadda kasar Iraqi ke kara daukar tsauraran matakai kan hada hadar kasuwanci da matafiya dake bi ta iyakokin kasashen sakamakon matsin lambar da kasar Amurka ke yi wa Bagadad na ta rage yawan musayar tattalin arziki da makwabciyarta ta gabas
Kasashen iran da Iraqi suna da huldar kasuwanci mai girma tsakaninsu, inda kayayyakin da iran ke fitarwa zuwa kasar ta larabawa ciki har da iskar gas da wutar lantarki suka kai na sama da dala biliyan 10 a duk shekara
Tawagar kwallon Kafa