A jiya Asabar 28 ga watan Nuwamba, sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun karfafa harhare kan kudancin kasar Lebanon, tare da amfani da makamai daban daban.
Shafin yanar gizo na labarai tashar talabijan ta Almayadeen tv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, a hare hare na jiya Asabar yahudawan sun yi amfani da makamai atulary, rusa gine gine, amfani da makaman kara masu cutarwa, da kuma haske shima mai cutarwa.
Labarin ya kara da cewa hare haren sun shafi yankunan Baraachit a laradin Bint Jbeil, sannan jiragen yakin yahudawa suka yi luguden wuta kan Adi Al-Saluqi kusa da garin Shaqra, da wani harin kan Kfar Tebnit.
Makaman atilary na yahudawan kuma sun yi barin wuta kan yankunan kudancin kasar ta Lebanon wadanda suka hada da bayan garin Baraachit, wadi Al-Khanazir, Ainatha, Kfar Tebnit, Wadi Al-Hujeir, Hadatha da kuma wajen garin Kfar Chouba, mansuri, Wadi Zibqin, Wadi al-Salouqi, Ali al-Taher, Majdal Zoun, Rashaf, Beit Yahoun, da kuma bayan garin Nabatieh al-Fawqa, Mayfadoun, da kuma Zawtar ta gabas.
Sai kuma a Khiam sun kai hare hare kan wani bangarensa. Daga karshe an jikarar tashin boma boma a kan Rub el-Thalathin, al-Qantara, Kfar Tebnit, Beit Yahoun, Zawtar al-Sharqiya, and Bint Jbeil.