Gwamnatin Kasar Pakistan ta tabbatar da cewa, ta tura sojoji zuwa kasar Saudia don taimakawa sojojin kasar Yakar Yemen wacce saudia take mamaye da ita tun shekara ta 2015.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto labarin da ke cewa kasar Pakistan ta tura sojoji zuwa kasar Saudia don taimakawa kasar a yakin da take fafatawa da kasar Yemen. Jami’an gwamnatin kasar Pakistan sun bayyana cewa, sun tura sojojin zuwa kasar Saudia ne saboda yarjeniyar da kasashe uku Saudia Pakistan da kuma Turkiyya suka rattabawa hannu a cikin watan Augustan da ya gabata, na tallafawa duk wata kasa wacce aka fermata da yaki daga cikin kasashen uku. Yarjeniya wacce suke kiranta Yarjeniyar Makka.
Pakistan bata bayyana yawan sojojin da ta tura zuwa kasar ta Saudia ba, amma ta tabbatar da cewa a cikin watan Afrilun da ya gabata ta aike da jiragen yaki zuwa kasar ta saudia, sannan ta kara da cewa, sojojinta zasu kare kasar Saudia ne kawai daga makaman na yemen amma ba zasu kaiwa huthawa hare hare ba.
Saudia ta mamaye kasar Yemen a cikin watan Maris na shekara ta 2015 da sunan maida tsohon shugaban kasar Yemen Abdu Rabbu Hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar, kuma ta hada kawancin kasashen Larabawa 10 don yin haka amma aka tsagaita wuta bayan yaki na shekaru 8 ba tare da samun nasara ba. Yaki ta sake barkewa tsakanin kasashen biyu a watan Yulin da ya gabata bayan da Yemen ta bukaci a dauke mata takunkuman tattalin arzikin da saudia ta dora mata shekaru 12 da suka gabata, wato tun shekara ta 2015.