An Karya Killacewar Amurka Ga Kasar Iran Ta Ruwa

Babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Iran Rear Admiral Shahram Irani ya bayyana cewa Iran ta karya killacewar da Amurka tayiwa Iran ta ruwa, sannan

Babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Iran Rear Admiral Shahram Irani ya bayyana cewa Iran ta karya killacewar da Amurka tayiwa Iran ta ruwa, sannan daga yanzu maganar toshe mashigar ruwa a wajen Iran ya zama tarihi har abada. Kuma dole ne makiyin su yi watsi da wannan Kalmar dangane da Iran har abada.

IKamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Irani yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a nan Tehran, ya kuma kara da cewa sojojin kasar Iran suna ra’ayin marigayi Imam Khomaini (q) wanda ya kafa jumhuriyar musulunci ta Iran na tabbatar da diyaucin kasar.

Irani ya kara da cewa mashigar ruwa ta Hurmuz zata ci gaba da rufewa har zuwa lokacinda makiya suka tabbatar da matsayin Iran suka kuma mutunta mutanen kasar.

The ceremony marked Navy Day, observed on November 28, and renewed the force’s allegiance to the ideals of the Islamic Republic’s founder as well as the Leader of the Islamic Revolution.

A wani labara kuma mutum guda ne ya bace a a lokacinda wani jirgin yakin Amurka samfurin Drones ya kai hari kan wani karamin kwale-kwale dauke da mutane 3, da misalign karfe 3.30 na daren Lahadi, a tsibirin SIrik. AN gano mutane biyu wadanda suke ji rauni amma matukin kwale-kwalen ya bace har yanzun ana ci gaba da nemansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted