Rahotanni sun bayyana cewa a gasar cin kofin kwallon kafa na bakin taku na yankin asiya da aka kammala a jiya asabar, tawagar kwallon kafa ta bakin teku ta iran ta samu nasarar dauke kofi a wasan karshe wato final da suka buga a kasar Thailand ta shekara ta 2026 inda ta lallasa kasar Japan da ci 3-1,
Kungiyar da Ali Naderi ke jagoranta ta nuna bajinta sosai a karo na biyu na wasan da aka yi a jiya asabar a filin wasa na ban nam khem beach arena dake kasar Thailand, bayan ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta bakin teku wadda fifa za ta shirya a shekara ta 2027 sakamakon kaiwa wasan karshe da ta yi
Har ila yau iran ta lashe kyaututtukan daidaikun yan wasa a gasar, inda aka zabi movahed mohammad pour a matsayin dan wasan da yafi kowa muhimmanci yayin da sayed mohammad dastan kuma ya samu kyautar gwarzon mai tsaron gida
Wanna shi ne karo na biyar da kasar iran ta dauke kofi a gasar kwallon bakin teku ta asiya, inda ta lashe kofin a shekara ta 2013, 2017,2023, da kuma 2025, kuma tuni ta shiga gaban japan a matsayin tawagar da tafi samun nasara a gasar, inda tayi nasarar dauke kofi a shekara ta 2025 bayan ta samu nasarar lallasa kasar oman da ci 8-1