Uganda: Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Yi Taro Akan Hanyoyin Bunkasa Noma A Nahiyar

Taron na Kampala an yi ne a matakai na uku, da ya fara da minsitocin harkokin noma na kasashen mambobi 55, sai na harkokin kasashen

Taron na Kampala an yi ne a matakai na uku, da ya fara da minsitocin harkokin noma na kasashen mambobi 55, sai na harkokin kasashen waje, sannan aka karkare da na shugabannin gwamnatocin kasashe mambobi.

An yin wannan taron ne da duk shekaru 10 da ake shata muhimman abubuwan da ake son cimmawa a fagen noma da kiwo.

Batun samarwa da nahiyar Afirkan abinci wani bababn kalubale ne da aka dade ana fuskanta. Abubuwan da suke kawo cikas kuma sun hada da sauyin yanayi, rikice-rikce, karuwar yawan jama’a a nahiyar da kuma koma baya na tattalin arziki.

Ministan aikin gona kuma mai kula da kamfanonin dabobi da kifi na kasar Uganda, Frank Tumbebaze  ne ya jagronci rubuta sabon daftarin da za a yi aiki da shi a nan gaba daga shekara ta 2026 zuwa 2035. Ya kuma fadawa manema labaru cewa:

“An kammala rubuta daftarin aiki a wannan taron na Kampala, don haka abinda ya saura shi ne yadda za a aiwatar da shi a aikace. Kuma ta wannan hanyar ta aiwatar ne za a sami tasiri mai ma’ana ga al’ummarmu ta Afrika. Don haka ya kamata mu yunkura, ya zama muna tafiya  kamar yadda ya dace domin samun cigaba.”

A cikin shekarun bayan nan, mutane miliyan 280 ne a nahiyar suke fuskantar yunwa, yayin da tsarin noman da ake aiki da shi ya gajiya wacce bai wa kowane bakin salati abinci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments