Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya bada sanarwan cewa a farkon shekara ta 2026 mai kamawa ne za’a fara aiwatar da kasha na biyu na yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza ta ranar 10 ga watan Octoban da ya gabata. Kuma kasar Turkiyya tana ganin kungiyar Hamas ta mika harkokin shugabancin yankin zuwa gwamnatin Falasdinawa ne.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudia ya bayyana cewa, a makon da ya gabata ne masu shiga tsakani a yarjeniyar wato Amurka, Qatar, Masar da Turkiyya suka hadu a birnin Miami na jihar Florida a kasar Amurka inda suka tattauna kan marhala na biyu na yarjeniyar.
A ranar 10 ga watan Octoban da ya gabata ne aka fara aiwatar da yarjeniyar, wanda ya rage kissan Falasdinawa, amma tun lokacinya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da 400, sannan kafin haka a yakin shekaru biyu da suka fafata yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da 70,000. A yayinda wasu 171,000 suka ji rauni.
Fidan ya gabatar da wannan bayanan ne a birnin Damascus na kasar Siriya a ziyarar aikin da ya kai kasar a cikin wannan makon.
Kwace iko daga hannun Hamas, kwance damararta da kuma januewar HKI daga karin yankunan gaza na daga cikin abinda marhala na biyu na yarjeniyar yake dauke da su. Amma kungiyar Hamas ta ce ba zata taba mika makamanta ba.