Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan Fidan ya bayyana cewa, makiya da suke tsoma baki a harkokin cikin gidan Iran, musamman abubuwan da suke faruwa a yanzu , za su ci kasa.
Ministan harkokin wajen kasar ta Turkiya da tashar talabijin din “Russia Today” ta yi hira da shi, ya ce; Amurka da ‘Yan sahayoniya suna tsoma baki a cikin abubuwan da suke faruwa a cikin Iran saboda su cimma manufofinsu,amma a karshe ba za su sami abinda suke so ba.