Tun Farkon Juyi Zuwa Yanzu Alkalai 77 Ne Su Ka Yi Shahada

Ma’aikatar sharia ta Iran ta sanar da cewa; daga farkon cin nasarar juyin musulunci na Iran zuwa yanzu adadin alkalan da su ka yi shahada

Ma’aikatar sharia ta Iran ta sanar da cewa; daga farkon cin nasarar juyin musulunci na Iran zuwa yanzu adadin alkalan da su ka yi shahada sun kai 77 saboda yadda su ke fada da cin hanci da rashawa da kuma ta’addanci.

Sanarawar ma’aikatar shariar ta kuma ce, a kodayaushe hanyar tabbatar da adalci tana hade da jini.

Daga cikin wadanda su ka yi shahada bayan cin nasarar juyin musulunci da akwai Ayatullah Dr. Sayyid Muhammad Baheshti wanda ya kasance shugaban kotun koli ta kasa, da kuma wasu mutane 72 a tare abokan aikinsa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta MKO masu adawa da juyin musulunci ce ta yi musu kisan gillar a ranar 28 ga watan Yuni na 1981.

Bugu da kari a 1998 an yi wa shahid Asadullah Lajibardi kisan gilla wanda ya kasance shugaban hukumar dake kula da gidajen kurkuku.

 Wasu daga cikin alkalan da su ka yi shahada sun hada da Ali Kudusi, da ya kasance babban mai shigar da kara, da shahid Musa Nuri Qaleh No, mai shigar da kara na gundumar Zabul, sai kuma shahid Ahmadi Maqdasi.

A jiya Asabar ne dai aka yi wa wasu alkalai biyu kisan gilla da su ne shahid Hajjatul-Islam Ali Razainy, da kuma Muhammad Maqisyeh.

Baya ga alkalai 77 da su ka yi shahada a tsawon tarihin juyin musulunci, wasu ma’aikatan ma’aikatar shari’a su 300 sun yi shahada a cikin wadannan shekarun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments