A jiya Lahadi ne mai Magana da yawun shugaban kasar Najeriya, Bola Tinibu ya rubuta a shafinsa na X cewa; Shugaba Buhari ya rasu a yau, a birnin London da misalin karfe 4;30″
A shekarar 2015 ne dai shugaba Buhari ya zama dan takara na farko wanda ya yi nasara akan shugaban kasar da yake kan kujerarar Mulki, Goodluck Jonatjan, a zaben da ake dauka mai inganci.
Buhari wanda janar din soja ne mai ritaya, ya Mulki Nigeria a shekaru 1980’s bayan da ya kifar da gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari.
A lokacin mulkinsa ya dauki matakan tsuke bakin aljihu da hakan ya jefa, mafi yawancin talakawan kasar cikin Karin talauci.
Mogoya bayansa suna daukarsa a matsayin wanda ya jagoranci fada da talauci da kuma rashin tsaro.
A lokacin mulkinsa ne a 2015 aka yi kisan kiyashin Zaria, wanda ya ci rayukan daruruwan ‘yan kungiyar Harkar musulunci a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaki