Joe Kent: Dole Ne Trump Ya Kawo Karshen Yaki Da Iran

Tsohon shugaban cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci na Amurka Joe Kent ya bayyana cewa dole ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kawo karshen yaki

Tsohon shugaban cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci na Amurka Joe Kent ya bayyana cewa dole ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kawo karshen yaki da kasar Iran ya kuma kori wasu daga cikin manya manyan jami’an gwamnatinsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kent yana fadar haka a jiya Jumma’a a rubutun da yayi mai suna “Dan kasa na gari”.

Kent ya kara da cewa sakamakon zaben ‘rabin wa’adin’ da aka gudanar a ranar talatan da ta gabata ya abbatar da cewa fiye da kashi 70% na mutanen Amurka basa goyon bayan yaki da Iran. Sannan basu yarda da dangantakar da ke tsakanin kasar da HKI ba.

Tsohon Jami’in CIA ya bukaci Trump ya sauke wasu daga cikin manya manyan Jami’an gwamnatinsa, wadanda suka hada da sakataren yaki pete Hegeth, daraktan CIA John Ratcliffe, sakataren harkokin waje Maco Rubio Jami’I mai kula da ma’aikata a fadar shugaban kasa Susie Wiles. Banda haka ya bukaci shugaban ya cire Mike Huckabee jakadan Amurka a HKI wanda yake aiki wa yahudawan fiye da Amurka. Ya bukaci Trump yam aye gurbinsu da wadanda zasu kawo karshen yakin. Ken y ace dole ne Trump ya amince da wasu bukatun Iran na dauke mata takunkuman tattalin arziki ficewa daga tekun farisa, da sauransu.

Share

2 2 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted