Tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekaru 100 a duniya, wanda ya sanya shi ne wani shugaban Amurka da ya fi tsawon rai bayan barin ofis.
Marigayin, wanda shi ne shugaban Amurka na 39 kuma daga jam’iyyar Democrat ya yi shugabanci daga Janairun 1977 zuwa Janairun 1981 bayan ya kada shugaba mai ci dan jam’iyyar Republican Gerald Ford a zaben 1976.
A lokacin shugabancinsa na wa’adin farko ne a 1978 aka cimma yarjejeniyar Camp David tsakanin Isra’ila da Masar.
A ‘yan shekarun nan, Carter ya fuskanci matsalolin lafiya da yawa ciki har da sankarar fata, wacce ta yadu zuwa hantarsa da kwakwalwarsa.
Carter ya shafe shekaru da dama yana ayyukan jin kai, ya kuma samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2002 saboda “kokarin da yake yi na samar da hanyoyin warware rikice-rikice a duniya.