Tsohon Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Cikin Kasa Da Mintuna 10 Iran Zata Mayar Da Martani

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Idan Amurka ta yi kuskuren kaddamar da hari kan Iran, to za ta fuskanci mayar da

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Idan Amurka ta yi kuskuren kaddamar da hari kan Iran, to za ta fuskanci mayar da martani cikin ƙasa da mintuna 10

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Iran kuma memba na Majalisar Shawarar Musulunci (Majalisar Dokoki) a yanzu, Manouchehr Mottaki, ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi wani abu da bai dace ba, za ta samu amsa cikin kasa da mintuna 10.

A lokacin wata hira da manema labarai, dan majalisar ya yi ikirarin cewa: Gazawar Yaƙin Kwanaki Goma Sha Biyu da abubuwan da suka faru a Iran kwanan nan suna daga cikin abubuwan da suka haifar da kokwanton Amurka kan kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tsohon jami’in diflomasiyyar ya lura cewa: “Idan Amurkawa ba su shiga yaƙi da Iran ba bayan Rashin cimma matsaya daya a  tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu, yanayin da ake ciki zai ci gaba kuma za Iran zata cimma burinta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted