Tsohon Kwamandan IRGC Ya Ce Boma-Boman HKI Na Zuwa Kanku Idan Kunki Samar da Kawance

Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan

Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, kasashen Saudiya, Turky da Iraki su jira randa boma-baman HKI zasu fada a kan kasashensu.

Rezai ya bayyana haka ne rana guda kafin a fara taron gaggawa na kasashen larabawa da musulmi a yau lahadi a birnin Doha na kasar Qatar.

Ya ce idan taron na Doha ya kasa samar da kawaice kasashen don fuskantar yahudawan , har aka waste, to kasashen Saudia da Iraki da turkiyya sun jira randa jiragen yakin HKI zasu yi luguden wata a kan kasashensu.

Rezai wanda ya kasance mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa ya zuwa yanzu HKI ta kai hare-hare ko kuma tana mamaye da wasu kasashen yankin wadanda suka hada da Lebanon, Yemen, Siriya , Qatar da kuma Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted