Tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki ya zargin wasu kasashe da kokarin ganin sun rusa gwamnatin Siriya
Shugaban gamayyar jam’iyyun daulatul-Qanun a kasar Iraki, Nuri al-Maliki ya jaddada wajibcin kare kasar Siriya da tabbatar da kasancewarta kasa daya dunkulalliya da wanzar da zaman lafiya da tsaronta da kuma kare ta daga duk wani harin ta’addanci daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi da suke aiki karkashin wasu kasashe masu dauke da mugun nufin kan kasar Siriya.
A hirar da aka gudanar da shi ta hanyar gidan talabiji dangane da halin da ake ciki a kasar Siriya a jiya Laraba, shugaban gamayyar jam’iyyun daulatul-Qanun ta kasar Iraki ya yi Allah wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan Siriya da kokarinsu na rusa hadin kan kasar.
Al-Maliki ya kara da cewa: Duk wata matsala da ta kunno kai a kasar Siriya musamman wargaza hadin kanta da kuma rusa zaman lafiyarta, shakka babu zasu yi mummunan tasiri a dukkan yankin Gabas ta Tsakiya, don haka wajibi ne a kan dukkanin kasashen yankin su dauki matakin kare kasar Siriya domin kasa ce mai muhimmanci, kuma faduwarta na nufin mamaye yankin baki daya.