A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu.
Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza.
Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can.
An kuma samu irin wannan halayyar ta yin kira a kawo karshen yakin a tsakanin likitocin soja su 100 sai kuma malaman jami’a su ma daruruwa.
Kiraye-kirayen da sojojii suke yi a HKI da na kwo karshen yakin Gaza da mayar da fursunonin yaki, ya bude wata sabuwar takaddama a tsakanin ‘yan siyasa.
Wasikar ta bude jayayya a tsakanin ‘yan sahayoniya akan cewa, Netanyahu yana ci gaba da yin yaki ne saboda maslahar kashin kansa.