Trump Zai Yi Ta Kara Yawan Kudaden Fito A Kan Turai Har Zuwa Lokacinda Zasu Mika Masa Greenland

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sha al-washin ci gaba da karawa kasashen turai kudaden fito har zuwa lokacinda zasu mika masa yankin Greenland na

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sha al-washin ci gaba da karawa kasashen turai kudaden fito har zuwa lokacinda zasu mika masa yankin Greenland na kasar  Denmark.

Tashar talabijan ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta kara da cewa shugaban ya rubuta a shafinsa na yanar gizo ‘Trump Social’ kan cewa a cikin watan Fabrayru mai kamawa kudaden fito na kashe 10% zai fara aiki a kan kasashen Denmark, Autria, Sweden, Faransa, Jamus, Burtaniya, Holand da kuma Finelanda.

Sannan ya kara da cewa kudaden fiton zasu karu zuwa kashi 25% a ranar daya ga watan Yunin wannan shekarar kuma zai ci gaba har zuwa lokacinda aka fahinci juna kan bukatar Amurka na mallakar yankin Greenlanda.

Kafin haka dai Trump ya bayyana cewa Amurka tana bukatar mallakan Greenlanda saboda tsaron kasarta. Banda haka tana da dimbin arziki na karkashin kasa mai yawa. Turawan dai sun aike da sojoji masu yawa zuwa kasar Denmark don kare Greendlanda daga mamayar Trump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted