Shugaban kasar Amurka Donal trump ya bada umurnin ga sojojin kasar su tsara yadda zasu kwace iko da Greenland.
Jaridar Daily Mail ta yau lahadi ta bata labarin cewa sojojin Amurka na musamman zasu fara shirin mamayar kasar Greenland amma babban hafsan hafsoshin sojojin kasar ya ki amincewa da shwarar mamayar kasar Greenlanda saboda ya sabawa dokokin kasa da kasa sannan mamayar baida goyon bayan majalisar dokokin kasar ta Amurka.
A ranar jumma’an da ta gabata shugaban kasar ta Amurka ya bayyana cewa dole ne sai ya kwace yankin Greenland na kasar Denmark don Amurka tana bukatar yankin don tsaronta. Idan bata yi ba kasashen China da Rasha zasu kwace yankin, sannan Amurka ba zata so ta zama makobciyar kasar Rasha da China ba.
Yace yana son ya yi cinikayya da mutanen Greenland ko Denmark amma idan sun ki amincewa ta so suna so ko basa so sai mun kwace ta.
Duk da cewa shugaban yana ambaton batun tsaro a matsayin dalilin da ya sa zai kwace Greenland sai dai bukatu mafi muhimmanci sune ma’adinai da arzikin karkashin kasa da suke kan Greenland.
Kasashen yamma da dama sun yi tir da wannan shirin na shugaba Trump, don alama ce ta wargajewar kungiyar tsaro ta NATO. A halin yanzu dai masu bawa shugaban shawara suna tattaunawa da shi kan yadda zai sami iko da yankin ko ta kaka.