Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka ta zartarwa da ke barazanar ƙarin haraji ga ƙasashen da ke ci gaba da yin huldar cinikayya tare da Iran, wanda kuma hakan ya zo ne jim kaɗan bayan da wakilan Iran da Amurka suka yi tattaunawa kai tsaye a birnin Muscat kan shirin makamashin nukiliya na Tehran da kuma rage takunkumi.
Umarnin, wanda aka sanya wa hannu a wnnan Juma’a, ya bayyana cewa Amurka za ta iya sanya haraji kan kayayyakin da aka shigo da su daga kowace ƙasa cikin Iran ta hanyar siya, ko kuma kasar da ta yi kaya daga kasar Iran, ko kuma wasu ayyuka daga Iran kai tsaye ko a bayan fage, Duk da cewa umarnin bai ƙayyade wani ƙayyadadde wasu kudi ba, amma dai ya ambaci da kashi 25 cikin ɗari a matsayin misali.
Trump a lokacin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One, ya sake nanata matsayinsa kan Iran, yana mai cewa bai kamata ta mallaki makaman nukiliya ba.
Babu wani martani nan take daga jami’an Iran kan wannan batu, waɗanda tuni suka yi watsi da zarge-zargen Washington da kawayenta kan ikirarin da suke na cewa tana neman mallakar makaman nukiliya ne a shirint.