Shugaba Bola Tinubu ya tafi Brazil don halartar taron shugabannin kasashen duniya 20 (G20) na karo na 19, wanda zai gudana a birnin Rio de Janeiro, na kasar Brazil.
Taron kasashen zai gudana ne a ranar 18 da 19 ga watan Nuwamba, 2024.
Tafiyar na zuwa ne bayan dawowarsa daga taron kasashen Larabawa da Musulunci da aka yi a kasar Saudiyya.
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Ya ce, “Gayyatar Shugaban Najeriya ya biyo bayan kiran Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, wanda shi ne Shugaban G20 na yanzu.
“Taron zai tattauna batutuwan duniya kamar yaki da yunwa da talauci, sauyi a bangaren makamashi, da gyaran harkokin mulkin duniya.”
Jigon taron shi ne “Gina Duniya Mai Adalci da Dorewa.”
Ana kuma sa ran Tinubu zai tattauna da shugabanni kasashe daban-daban domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Zai samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministocin Harkokin Waje da na Noma.