Hemomin ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa A Gaza Sun Fada Cikin Ambaliyar Ruwa

A dai dai lokacinda HKI take ci gaba da hana shigowar kayakin agaji cikin zirin gaza, wanda ya sabawa yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da

A dai dai lokacinda HKI take ci gaba da hana shigowar kayakin agaji cikin zirin gaza, wanda ya sabawa yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da suka cimma a cikin watan Octoban da ya gabata, ambaliyar ruwa ta shiga dukkan tentuna falasdinawa yan gudun hijira a yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto magajin garin birnin Gaza Yahya Al-Sarraj yana cewa tun lokacinda aka fara ruwan sama da iska mai karfi a gaza a ranar Jumma’a wasu falasdinawa yan gudun hijira sun rasa tantunansu don haka a waje karkashin ruwan sama da iska suke kwana. A kuma dai dai lokacinda iska yake kara sanyi.

Labarin ya kara da cewa a jiya asabar an yi ruwa da iska mai yawa, wanda kara sanyin a yankin tare da ruwan sama mai yawa, da kuma Iska. Kuma ana saran wannan halin zai ci gaba har zuwa ranar Laraba. Sannan a mako na gaba ma, ana saran wani irinsa zai sake shigowa yankin.

Majiyar Falasdinawa ta bayyana cewa HKI ta rufe dukkan kofofin shiga Gaza, sun kuma hana shigar kayakin agaji wadanda suka hada da tentuna masu inganci da kerarrun gidaje na wucin gadi da kuma kayakin abinci isassu da magunguna. Yankin. Wanda ya kuma ya sabawa yarjeniyar da aka cimma da ita a watan Octoban da ya gabata.  HKI ta kashe Falasdinawa kimani 70,000 a cikin shekaru 2 daga suka gabata sannan suna ci gaba da kashewa hatta bayan yarjeniyar tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted