A yammacin jiya Asabar ne aka gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv don nuna adawa da yakin da Harmtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran Isra’ila suka rawaito.
Daga cikin jiga-jigan mutane da suka halarci zanga-zangar har da memba na Knesset Ofer Cassif, wanda ya rubuta cewa, “A daina kisan kare dangi, ku dakatar da yakin.” Masu zanga-zangar sun daga tutoci da aka rubta cewa, “Ku masu kashe yara, ku daina kisan kare dangi a Gaza.”
A wani lamari makamancin haka, mazauna yankin sun gudanar da zanga-zangar adawa da ministan tsaron ciki gida, Itamar Ben-Gvir, a lokacin da yake cikin wata majami’a.
Rikici baki ya barke tsakaninsa da daya daga cikin masu zanga-zangar wanda yake nuna adawa da matsayar da Ben-Gvir ya dauka kan batun musayar fursunoni.
Daya daga cikin masu zanga-zangar ya yi jawabi a gaban Ben-Gvir, inda ya ce, “Kai dan ta’adda ne da ya kamata a yanke wa hukuncin kisa, kuma kai mai kisan fursunoni ne, kai ne ka dakile yarjejeniyar a kan wane dalili?” kamar dai yadda kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito.
Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin jami’in soji a bataliya ta 75, ya zargi Ben-Gvir da gujewa aikin soja, kuma bai taba yin kwana daya a cikin sojojin Isra’ila ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila suka fara wani mataki na biyu na Operation Gideon da ke mayar da hankali kan mamaye birnin Gaza, tun bayan da Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da shirin mamayar.