Tattunawar Iran, Turkiyya, Masar Da Saudiyya Kan Ci Gaban Da Aka Samu A Tattaunawar Muscat

Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Turkiyya, Masar da Saudiyya kan ci gaban da aka samu a tattaunawar Muscat Ministan Harkokin

Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Turkiyya, Masar da Saudiyya kan ci gaban da aka samu a tattaunawar Muscat

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tattaunawa ta wayar tarho daban-daban da takwarorinsa na Turkiyya, Hakan Fidan; Masar, Badr Abdel-Aty; da Saudiyya, Faisal bin Farhan.

A cikin waɗannan kiraye-kiraye daban-daban, Araqchi ya yi wa takwarorinsa bayani game da sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar da ba na kai tsaye ba a Muscat, inda ya bayyana tattaunawar a matsayin kyakkyawar farawa tare da jaddada buƙatar kawar da shakku game da niyya da manufofin ɓangaren Amurka.

Ministocin sun jaddada mahimmancin ci gaba da tattaunawar don tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin.

A halin yanzu, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, a cikin wani taron manema labarai, ya tabbatar da cewa babu wata barazanar yaƙi kai tsaye tsakanin Amurka da Iran, yana mai jaddada sha’awar ƙasarsa ta amfani da duk hanyoyin da ake da su don hana yiwuwar yaƙi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted