Tattaunawar Muscat : Araghchi ya tattauna da takwarorinsa na Turkiyya, Masar, Da Saudiyya

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Turkiyya, Masar, Da Saudiyya domin yi musu bayani kan sabbin abubuwan da

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Turkiyya, Masar, Da Saudiyya domin yi musu bayani kan sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar da aka gudanar tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka, a Muscat.

Seyyed Abbas Araghchi ya bayyana tattaunawar a matsayin kyakkyawan mafari.  

A nasu bangaren, ministocin harkokin wajen kasashen yankin sun yi maraba da fara tattaunawar Muscat kuma sun jaddada muhimmancin ci gaba da wadannan tattaunawa don cimma matsaya ta siyasa da diflomasiyya da kuma hana duk wani tashin hankali.

Sun kuma bayyana cewa nasarar wadannan tattaunawar tana da matukar muhimmanci ga kwanciyar hankali da tsaron yankin.

Ya jaddada bukatar gaggawa ta sake gina aminci yayin da yake bayyana shakkun Iran game da manufofin Amurka, musamman idan aka yi la’akari da takunkumin da take ci gaba da kakabawa Iran da kuma barazanar yaki.  

An gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka, wanda Oman ta jagoranta, a babban birnin Oman a ranar Juma’a, karkashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Oman Badr bin Hamad Al Busaidi.

Iran ta dage kan cewa tana da hakkin malakar fasahar nukiliya da kuma tace uranium.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted