Kungiyar tarayyar Turai ta yi allawadai da gwamnatin kasar Poaland bayan da ta gayyaci Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu zuwa bukukuwan entar da sansanin fursinoni na Nazi na “Auschwitz” karo na 80Th a cikin wannan sabuwar shekara ta 2025, ba tare da jin tsoron za’a kama shi ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban kakakin kungiyar EU Anwar Al-Aoun ta na fadar cewa, yin watsi da sammacin kotun ta kasa da kasa ba dai-dai ba ne, sannan kasashen tarayyar Turai gaba daya sun sanyawa yarjeniyar Roma wacce ta kafa kotun ta ICC a shekara ta 2002, don haka bai kamata kasar Polant ta yi watsi da umurnin kotun ba.
A cikin watan Nuwamban da ta gabata ce, kotun ta ICC ta fidda sammacin kama firai ministan HKI Banyamin Natanyahu da kuma tsohon ministan tsaronsa Yaov Galant saboda zargin aikata laifukan yaki a Gaza daga cikin watan Octoban shekara ta 2023 zuwa watan mayu na shekarar ta 2024.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa kasar Poland tana son karfafa dangantaka da HKI, kuma wannan dama ce ta yin haka, don haka ne ta yi watsi da sammacin kotun ta ICC.