Shugaban Tarayya Afirka AU ,Ali Youssouf, ya bukaci kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa Alummar Falasɗinu.
Yayin jawabinsa a taron kungiyar karo na 39 da yanzu haka ke gudana a birnin Addis Abeba na Ethiopia, Youssouf, ya yi kira ga kasashen duniya da su kalli mawuyacin halin da al’ummar Falasdinu ke ciki.
A cewar ma’aikatar lafiyar Falasdinu, mutum kusan dubu 72 sojojin Isra’ila suka kashe tun fara yakinsu da Kungiyar Hamas a watan Octoban 2023.
Haka ma Shugaban kungiyar ta AU ya dauko batun yake-yaken da ke faruwa a ƙasashen Sudan,da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Somalia da kuma wasu ƙasashen yankin Sahel yana mai bayyana takaici kan yadda aka gaza cimma zaman lafiya a wadanan rikice-rikicen.
dukkan shugabanin Afirka da su ka halarci taron bakinsu yazo daya wajan yin Allah-wadai da shishigin ƙasashen yammacin duniya a harakokin cikin gidan nahiyar.