Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a yankin Damascus ya karu zuwa 5, yayin da wasu ma’aikatan ma’aikatar tsaron kasar Syria suka samu raunuka, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syria.
Cibiyar sa ido ta kasar Syria ta sanar a yammacin jiya Talata cewa, hare-haren biyu an kai su ne a yankin al-Kiswah da ke yankin Damascus, kusa da hanyar Suwayda, tare da raunata wasu sojojin sabuwar gwamnatin kasar ta Syria, wanda suka kasance mambobin kungiyar Hay’at Tahrir al-Sham mai alaka da kungiyar da Aqaida.
Majiyoyin cikin gida sun kuma tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a wani shingen binciken sojojin sabuwar gwamnatin da na jami’an tsaron cikin gida da ke birnin al-Sanamayn da ke arewacin Daraa.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kara zafafa hare-harenta da keta hurumin kasar Siriya, musamman kan iyaka da tuddan Golan da ta mamaye.
Bayan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan kan fagen siyasar kasar Siriya, Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Siriya (SANA) ya bayar da rahoton wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad al-Sheibani da tawagar Isra’ila a birnin Paris na kasar Faransa, wanda shi ne karon farko da aka taba wata gudanar da wata ganawa a tasakanin jami’an Syria da Isra’ila.