Firaministan Sudan Kamil Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya goyi bayan shirin zaman lafiya na kawo karshen mummunan yakin da kasar ke fama da shi.
Da yake jawabi a birnin New York, Mista Idris ya ce : Dole ne mu ayyana cikakken tsagaita wuta, karƙashin kulawar hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka, da Ƙungiyar kasashen Larabawa, da janye ‘yan tawaye daga yankunan da suka mamaye,” in ji Firaministan Sudan, wanda ke jagorantar gwamnatin rikon kwarya ta Sudan.
Yaki ya barke a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF), mai karfi a yamma da sassan kudancin kasar.
Yakin ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40,000 sannan miliyoyin sun rasa matsugunansu.